MAI KARFI HELP

Technology Made Easy

Yadda Ake Gano Wayar Android Da Ta Ɓace

Idan wayarka ta ɓace, kada ka firgita. Google yana da wani tsarin da zai iya taimaka maka gano wayarka, kulle ta ko goge bayananta.

Abubuwan Da Ake Bukata

Mataki Na Farko

Buɗe browser a wata waya ko kwamfuta.

Shiga shafin Google Find Hub ta wannan adireshin:

Google Find Hub

Mataki Na Biyu

Shiga da Google Account ɗin da yake cikin wayar da ta ɓace.

Mataki Na Uku

Zaɓi wayarka daga jerin na'urorin da suka bayyana. Idan Google ya iya gano ta, zai nuna maka wurin da take ko wurin da aka gan ta na ƙarshe.

Mataki Na Huɗu

Za ka iya amfani da waɗannan zaɓuɓɓuka:

MUHIMMIN GARGADI

Kada ka bai wa wani mutum password ko OTP ɗinka. Idan wayarka ta ɓace, ka kuma sanar da kamfanin layinka domin dakatar da SIM idan ya zama dole.

Ka sani: ba koyaushe ne za a iya gano waya ba. Dole ne na'urar ta cika sharuddan Google.


Komawa Homepage